Da Ɗumi Ɗuminsa! Kotu Ta Umurci AGF Malami Da Ya Cire Sashe Na 84(12) Daga Cikin Dokar Zabe

Alfijr ta rawaito babbar kotun tarayya da ke zama a Umuahia, jihar Abia ta umurci babban lauyan gwamnatin tarayya da ya gaggauta soke sashe na 84 (12) na sabuwar dokar zabe.

Mai shari’a Evelyn Anyadike, ta kuma umurci babban mai shari’a na tarayya kuma ministan shari’a Abubakar Malami da ya cire wannan sashe daga cikin dokar.

Sashin da ke bukatar masu rike da mukaman siyasa da ke neman mukaman zabe da su yi murabus kwanaki 30 kafin zaben, ya bayyana cewa “Babu wani mukami na siyasa a kowane mataki da zai zama wakili mai kada kuri’a ko a zabe shi a babban taron ko taron kowace jam’iyyar siyasa domin nada ‘yan takara., a kowane zabe.

Alfijr

A halin yanzu, kafin a yi wa kowane sashe na Dokar Zaɓe tabarbarewa, dole ne dokar ta bi tsarin doka tare da komawa ga shugaban ƙasa don sake amincewa da shi.