Alfijr
Alfijr ta rawaito kungiyar mata masu zaman kansu (karuwai) reshen Zaria dake jihar Kaduna, sun yi Allah wadai da sabuwar dabi’ar da mazaje suka shigo musu da ita, wadda hakan ta sa suka sanar da cewar akwai yiwuwar su tsunduma yajin aiki na wani lokaci a matsayin jan kunne ga mazaje masu nemansu.
Karuwan sun koka kan yadda mazaje ke zabtare musu farashi idan sun yi magana sai mazaje su ce musu sun kashe kudi da yawa wajen abin hawa saboda karancin man fetir.
Kungiyar ta yi kira ga membobin ta da su kauracewa gidajen shakatawa, otal-otal da duk wajen cin abinci domin tafiya yajin aikin gargadi.
Alfijr
Kamar yadda Rariya ta wallafa