Rasha ta haramta wa jiragen ƙasashe 36 shiga ƙasarta

Alfijr

Alfijr ta rawaito Rasha ta sanar da haramtawa jirage daga ƙasashe duniya 36 shiga ƙasarta

Alfijr

Kasashen sun ƙunshi Birtaniya da Jamus da Spain da Italiya da Canada.

Wannan na zuwa bayan matakin da Tarayyar Turai ta ɗauka na haramta wa jiragenta ratsawa sararin samaniyar mambobin ƙungiyar tarayyar Turai.

Alfijr

Birtaniya kuma ta haramta wa Aeroflot sauka cikin Birtaniya, wanda ya sa Rasha ta mayar da martani na haramta wa jiragen Birtaniya shiga ƙasarta.

Kamar yadda BBC Hausa suka rawaito.

Slide Up
x