BBC Ta Saka Gasar Rera Waka Ga Duk Mai Sha awar Shiga

Alfijir

An bude gasar ce ga masu shekara 18 zuwa sama domin karfafa wa matasa gwiwa wajen baje-kolin irin fasahar da Allah ya huwace musu wajen waka a harshen Hausa.

Za a iya shiga wannan gasa a daidaiku ko kuma a kungiyance (amma kada a wuce mutum uku) kuma dole ne kowanne mutum ya kai shekara 18.

Za a samu damar shiga gasar ne ta hanyar cike fom domin shigar da bayanai a wannan adireshin https://www.bbc.co.uk/send/u101733987

Alfijir

Sannan kuma sai a aike da wakar a tsarin sauti na MP3.

Bai kamata tsayin waka ya wuce minti biyar ba, kuma sau daya za a iya shiga gasar saboda haka duk wanda zai shiga (mutum daya ko hadaka) ya kamata ya karanta ka’idojin kafin ya aike da sakon waka.

An bude gasar da karfe 00:01 agogon GMT ranar 3 ga watan Fabrairu kuma za a kulle da karfe 23:59 agogon GMT na ranar 16 ga watan Fabrairu.

Alfijir

BBC za ta zabi wakokin da suka yi fice guda 30 kafin daga bisani alkalan gasar su zabi guda 15 da suka yi fice inda kuma za su kwalkwale da zaben uku da suka zamo zakaru.

BBC za ta tuntubi masu wakoki uku da suka zamo zakaru ne kawai, domin mika musu kyautuka yayin bikin cika sashen shekara 65, a birnin Abuja, Najeriya.

Domin samun karin bayani kan shiga gasar sai a ziyarci shafinmu na bbchausa.com.

BBC za ta zabi fitattun wakoki guda 30 wadanda da suka dace da ka’idojin shigar gasar kamar haka:

  • Bayyana turken waka kuru-kuru; cikar BBC Hausa shekara 65 da watsa shirye-shirye;
  • Dacewar kananan sakonnin waka da turken waka;
  • Dole waka ta mayar da hankali kan tarihi da shirye-shiryen BBC Hausa da rawar da take takawa wajen yada harshe da al’adun Hausawa a duniya;
  • Dacewar Rauji (karin murya ko amsa-amon murya) da kidan wakar da aka rera, Amfani da harshe da azanci da fasahar waka;
  • Amfani da dabarun janhankali ko adon waka.

Alfijir

Za a sanar da mutum uku da suka yi nasarar zamowa na daya da na biyu da na uku yayin taron karramawa a birnin Abuja, Najeriya, a cikin shekarar 2022. Za a wallafa lokacin da za a yi wannan bikin na karramawa a shafin bbchausa.com.

BBC za ta yi amfani da wakokin da suka zamo zakaru guda uku ta hanyar watsawa a rediyo da intanet da soshiyal midiya da twitter da Instagram da Facebook.

Idan aka watsa wadannan wakoki naku za su iya zama har abada a shafukan BBC na intanet sannan kuma za a iya sake amfani da su a rediyo a nan gaba idan bukatar hakan ta taso

Slide Up
x