Wani Jirgi Ya Makale Da Matafiyi Daga Kano Zuwa Lagos Tsawon Kwana 9

Alfijr

Alfijir ta rawaito, wani mai suna Yomi A shafinsa na Twitter, ranar Talata ya bayyana cewa, mun hau wani jirgin kasa tun jiya 31 ga watan Janairu da misalin karfe 9 daga Kano muka nufi Lagos kuma har yanzu ba mu isa Zariya ba, kuma ma aikatan jirgin sun yi watsi da mu a cikin daji na kusan awanni 18, ko la akari da yadda masu garkuwa da mutane ba su yi ba

A cikin wani faifan bidiyo da aka saka a ranar Laraba, ya ce, “Kusan ashirin da hudu a yanzu, mun makale a tsakar daji, dubi inda mutane ke tsaye, ban ma san abin da zan yi ba a yanzu. Mun makale a tsakiyar daji babu Jama’a kuna bukatar ku magance wannan matsalar da wuri-wuri. Inji Yomi a shafinsa na Twitter yomicriminal

Alfijir

Yomi, ya koka kan yadda hukumar jirgin kasa ta yi shakulatin bangaro da su.

Slide Up
x