Da Dumi Duminsa: Gwamna Yusuf ya sauke Kwamishinan Ma’aikatar Zuba Jari, Kasuwanci da Masana’antu da nan take.

FB IMG 1774483085694

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya amince da sauke Alhaji Shehu Wada Sagagi daga mukaminsa na Kwamishinan Ma’aikatar Zuba Jari, Kasuwanci da Masana’antu da nan take.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya sanya wa hannu.

Wannan mataki ya fara aiki nan take.

Gwamnan ya umarci Alhaji Sagagi da ya mika ragamar ma’aikatar ga Babban Sakataren ma’aikatar.

Ana sa ran zai kammala mika ragamar aiki zuwa gobe da safe.

Hakazalika Gwamna Yusuf ya gode masa bisa gudunmawar da ya bayar a lokacin da yake rike da mukamin.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *