Shugaban Kwamitin Gudanarwa na Bankin Lamuni na Tarayya (FMBN), Nasiru Gawuna, ya yi murabus daga mukaminsa. hakan na zuwa ne yayin da Gawuna ya kammala shirinsa na sauya sheƙa tare da tsohon gwamnan Kano, Rabiu Kwankwaso, kuma ana sa ran zai koma jam’iyyar ADC a gobe Talata.
A cikin wasikar murabus da ya rubuta mai kwanan wata 27 ga Maris, 2026, tsohon ɗan takarar gwamna na jam’iyyar APC ya ce matakin nasa zai fara aiki nan take, kuma ya yi daidai da umarnin Shugaban Ƙasa domin tabbatar da bin dokokin zaɓe yayin da ake tunkarar kakar zaɓe mai zuwa.
Ya kuma bayyana matuƙar godiyarsa ga Shugaba Bola Tinubu bisa damar da ya ba shi na yin hidima, inda ya bayyana wa’adinsa a matsayin wata dama ta ba da gudummawa ga ci gaba da bunƙasar Bankin Lamuni na Gidaje na Tarayya da kuma ƙasar baki ɗaya.
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t