Alfijr
Alfijr ta rawaito hukumar shirya jarabawa ta kasa (NECO) ta fitar da sakamakon jarrabawar kammala sakandare ta shekarar 2021 (SSCE)
Alfijr
Bisa sakamakon da aka fitar, jimillar mutane 29,342, wanda ke nuna kashi 62.59 na wadanda suka zana jarrabawar sun samu maki biyar (5) da sama da haka, wadanda suka hada da Turanci da Lissafi.
Da yake sanar da sakamakon a Minna ranar Alhamis, magatakarda kuma shugaban hukumar ta NECO, Farfesa Dantani Ibrahim Wushishi, ya ce an fitar da sakamakon ne bayan kwanaki sittin da hudu (64) a karshen takardar da aka rubuta.
Alfijr
Ya kuma bayyana cewa, an samu raguwa sosai a yawan laifukan da aka saba yi a jarrabawa.
Shugaban NECO ya ce: “Yawan wadanda suka yi rijistar jarrabawar sun kai kimanin 47, 916. “Yawan wadanda suka zana jarabawar Ingilishi sun kai 45,821 daga cikinsu 36,116, wanda ke nuna kashi 78.82 cikin 100 ne suka samu Credit kuma sama da haka.
Alfijr
Daliabai 45,756 ne suka zana lissafi, daga cikin su 35,706, wanda ke wakiltar kashi 78.04 cikin 100 ne suka samu Credit kuma sama da haka.
Yawan dalibai da suka samu maki biyar (5) da sama da haka, da suka hada da Ingilishi da Lissafi sun kai 29,342, wanda ke wakiltar kashi 62.59 cikin 100 .
Alfijr
A daya bangaren kuma, dalibai 37,991, wadanda ke wakiltar kashi 81.04 cikin 100 sun samu maki biyar (5) da sama, ba tare da la’akari da Turanci da Lissafi ba.
“Yawan daliabai da aka yi rajista don nau’ikan laifuka daban-daban a cikin 2021 ya kai 4,454, sabanin 6,465 a 2020, wanda ke nuna raguwar yawan laifuka.
Alfijr
Da yake karin haske, Farfesa Dantani ya ce dalibai za su iya samun sakamakonsu a shafin yanar gizon NECO na www.neco.gov.ng, ta hanyar amfani da lambobin rajistar jarrabawar.
Yayin da yake cewa majalisar ta fara aiwatar da shirye-shirye daban-daban na sake fasalin hukumar jarabawar don samun ingantacciyar aiki, shugaban NECO ya yabawa shugaban kasa Muhammadu Buhari da ministocin ilimi guda biyu bisa gagarumin goyon baya.
Alfijr
Ina godiya ga shugaban kasa kuma babban kwamandan tarayyar Najeriya bisa goyon bayansa da taimakonsa wajen aiwatar da aikin majalisar. “Ina kuma godiya ga Mai girma Ministan Ilimi, Malam Adamu Adamu da Karamin Ministan Ilimi, Honourable Chukwuemeka Nwajiuba bisa goyon bayan da suka ba su.
Haka kuma ga Shugaban Hukumar da ‘yan kwamitin gudanarwa a karkashin jagorancin Dr Abubakar Siddique Mohammed bisa goyon bayansu da ja-goranci. “Ina kuma son godiya ga ‘yan majalisar dokokin kasar da suka ci gaba da tallafawa majalisar, ta hanyar kwamitocin sa ido,” in ji shi.