Da Yawun Gwamnati Ake Gine-Ginen Ba Bisa Ka’ida Ba A Kano! In Ji Lauya Abba Hikima

rawaito kwararrun lauyan nan mai fafutukar kare shakkin ɗan adam a jihar Kano, Abba Hikima ya musamsanta wani Jami in gwamnati da ya ce ba da sanin gwamnatin Kano ake wadannan gine-ginen ba

Alfijr Labarai

Jami in wanda ya tattauna da kafar BBC Hausa ya gayawa duniya cewa ba su da sanin izinin gine-ginen ba bisa ka ida ba.

Abba ya ce wata bakwai da suka gabata shi da kansa ya kai gwamnatin jihar Kano kara kan tursasata ta bude magudanun ruwa da yanyoyi da sauran gine-ginen da ake ba bisa ka’ida ba.

Ya ƙara da cewar akwai kara da ya kai gwamnatin  da hukumar kanupda kan hana wani gini shaguna a kan titin Katsina Road dake jihar saboda rashin dacewa

Haka zaliika, ginin layin Ta ambu da Da sauran hanyoyin ruwa da ake tarewa an san cewar dole sai hakan sai ta faru, domin ruwa ba a tare masa hanya.

  Alfijr Labarai

Idan kuka kalla duk gine-ginen da ake yi kama da Katsina rd Kantin Kwari, masallacin Fagge, masallacin Idi da sauran gine ginen da ake ana yinsu ne bisa rashin tsari da inganci, in ji shi

Ina mai bada shawarar da azo a duba wadannan gine-ginen da sauri, idan ba haka ba wallahi akwai wasu da zasu Ruguje nan gaba kadan 

Ya kara da cewa duk kanin wadannan masifu da suke ta faruwa jihar laifin gwamnati ne, domin ita take da hakkin magance komai 

Kamar yadda Abban ya wallafa a shafinsa na Facebook