Alfijr ta rawaito Kotu ta kwace wasu kadarori 14 da ke da alaka da Gwamnan Najeriya.
A kalla kadarori 14 da ake zargin Gwamnan Jihar Kogi Yahaya Bello ne, wanda babbar Kotun Tarayya da ke Legas ta kama su.
A hukuncin da ya yanke a ranar Laraba, alkalin kotun mai shari’a Nicholas Oweibo, ya bayar da umarnin kwace kadarorin da ke Legas da Abuja da kuma Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) na wucin gadi ga gwamnatin tarayyar Najeriya.
Mai shari’a Oweibo ya kuma bayar da umarnin a karbe Naira miliyan 400 da ake zargi da alaka da jihar tare da kwato daga hannun wani Aminu Falala.
Alkalin ya bayar da umarnin ne bayan ya ji dadin wata takardar da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC) ta gabatar a gabansa.
Kotu ta ba da umarnin kwace wasu kadarori 14 a Abuja A yayin gabatar da karar, lauyan EFCC, Rotimi Oyedepo (SAN), ya yi ikirarin cewa kadarorin da suka hada da na ginin mafi tsayi a duniya, Burj Khalifa da ke Dubai, UAE, ana zarginsu da kasancewar samunsu daga haramtattun ayyuka.
Oyedepo ya kuma shaida wa Kotun cewa Naira miliyan 400 da ake zargin an same su ne daga wata haramtacciyar hanya da nufin mallakar Plot No. 1224 Bishop Oluwole Street, Victoria Island, Legas.
Alkalin, ya umurci hukumar yaki da cin hanci da rashawa da ta buga wannan umarni a cikin kwanaki 14 domin duk mai sha’awar ya nuna dalilin da ya sa bai kamata a ba da umarnin kwacewa har abada ba.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇
Really appreciate u