Dan Aikin Gida Ya ɗirkawa Yar Mai Gidansa Ciki, Ya Kuma Koneta ƙurmus

Alfijr ta rawaito Munzali ado ya ɗirkawa yarinyar ciki sannan ya hada baki da mahaifiyarta domin kaita jihar Gambe don a zubar da cikin

Alfijr Labarai

Kakakin hukumar, yan sandan jihar SP Ahmed Wakil, a ranar Asabar 13 ga watan Agusta, 2022, yace an cafke wasu mutum biyu ciki har da matar da ta bayar da abin zubar da cikin. 

 Wakil, ya ce bayan samun nasarar zubar da cikin mai wata huɗu, wanda ake zargin da abokin sa sun maƙare yarinyar, sannan suka ƙona jikinta ƙurmus tare da birne ta a cikin wani ƙaramin rami a cikin daji.

Kakakin ƴan sandan yace, mahaifin yarinyar wanda ya lura da cewa yarinyar sa ta ɓace kuma yana zargin ɗan aikin gidan da abokin sa, sai ya miƙa rahoton lamarin a ofishin ƴan sanda na Alkaleri.

Alfijr Labarai

A ranar 10/08/2022 da misalin ƙarfe 9 na safe, wani Alhaji Danladi Mohammed, daga ƙauyen Mai’ari Arewa Pali, ya shigar da ƙorafi a ofishin ƴan sanda na Alkaleri, cewa a ranar 04/08/2022 ɗiyar sa mai suna Safiya Alhaji Danladi ƴar shekara 13, ta bar gida inda akayi zargin ta ɓace sannan yana zargin cewa ɗan aikin gidan sa mai suna Munkaila Ado mai shekara 27 da wani Muazu Umaru mai shekara 35, sune waɗanda yake zargin sanin inda ƴar sa ta ɓace. Inji shi

Nan da nan aka fara gudanar da bincike, DPO na Alkaleri yaje wurin da aka birne yarinyar sannan aka tono ta inda aka kai ta babban asibitin Alkaleri, inda likita ya tabbatar da ta rasu

Alfijr Labarai

A yayin da ake masa tambayoyi, wanda ake zargin ya bayyana cewa yarinyar budurwar sa ce kuma tana ɗauke da cikin wata huɗu da sanin mahaifiyar ta amma mahaifin ta Alhaji Danladi Mohammed bai sanda cikin ba.

Ɗan aikin gidan ya haɗa baki da mahaifiyar yarinyar suka bata maganin zubar da cikin Wanda ya kaiga rasa rai.

Slide Up
x