Jigo A  Gidan  Shekarau  Ya Shiga Jerin Sunayen Kwamishinonin Ganduje

Alfijr Labarai

  Wani babban na hannun daman tsohon Gwamnan Kano Sanata Ibrahim Shekarau Malam Garba Yusuf Abubakar ya shiga jerin sunayen wadanda Gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya aike wa majalisar dokokin jihar domin tantance su a matsayin kwamishinonin.

Alfijr Labarai

Kafin gudanar da zaben fidda gwani na jam’iyyun siyasar Najeriya wasu kwamishinonin sun yi murabus daga majalisar  zartarwar Gwamna Abdullahi Umar Ganduje.

Kwamishinonin da Gwamnan ya aike  sun hada da

Hon. Ibrahim Dan’azumi Gwarzo Hon. Abdulhalim Liman Dan Maliki Hon. Lamin Sani Zawiyya Hon. Ya’u Abdullahi Yanshana Hon. Garba Yusif Abubakar Dr. Yusif Jibril Rurum Hon. Adamu Abdu Panda Hon Saleh Kausani.

Garba Yusuf Abubakar yana daya daga cikin jiga-jigan gwamnatin Gwamna Malam Ibrahim Shekarau na tsawon shekaru 8 daga 2003 zuwa 2011 kuma ya rike ma’aikatar yada labarai da tsare-tsare, da ta filaye da ma’aikatar kudi ta jiha tsawon shekaru  a mulkin Malam Ibrahim Shekarau.

Alfijr Labarai

Mutane ba su taba tunanin Garba Yusuf Abubakar zai yi karo da babban amininsa kuma aminin sa tsawon shekaru da dama.

Garba Yusuf Abubakar wanda aka fi sani da Garba Izala a Kano saboda alakarsa da Jama’atu Izalatul Bidia Wa ikamatussunnah.

Sakamakon rikicin cikin gida Malam Ibrahim Shekarau yanzu sanata mai wakiltar Kano ta tsakiya ya koma jam’iyyar New Nigeria People’s Party ta Rabi’u Musa Kwankwaso kuma tun daga nan ya ci tikitin takarar Sanata na jam’iyyar a zaben 2023.

Alfijr Labarai

Malam Ibrahim Shekarau yanzu sanata mai wakiltar Kano ta tsakiya ya koma jam’iyyar Rabi’u Musa Kwankwaso’s New Nigeria People’s Party kuma tun daga nan ya ci tikitin takarar sanata na jam’iyyar a zaben 2023.

Slide Up
x