Alfijr ta rawaito Karim Benzema, dan wasan gaba na Real Madrid kuma kyaftin, an ba shi kyautar Ballon d’Or na 2022.
Alfijr Labarai
Dan wasan na Faransa ya doke Sadio Mane da Robert Lewandowski inda ya lashe zawarcin gong a bikin da aka gudanar a Théâtre du Chatelet a birnin Paris na kasar Faransa a yammacin ranar Litinin.
Benzema ya jagoranci Real Madrid ta lashe kofin zakarun Turai na UCL karo na 14, inda ya ci kwallaye 15 a kakar wasa ta bana.
Haka kuma an ba shi kyautar gwarzon dan wasan UCL a kakar wasa ta bana saboda yadda ya taka rawar gani a gasar da ya jagoranci Madrid zuwa wasan karshe.
Kazalika Benzema ya zaburar da Galacticos wajen samun nasarar lashe gasar La Liga ta Spain karo na 35, inda ya kammala gasar a matsayin wanda ya fi zura kwallaye 27.
Alfijr Labarai
Mane ya lashe Kofin Socrates – sabuwar lambar yabo – saboda kokarinsa na jin ƙai a ƙasar Senegal.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller