DSS Ta Bayar Da Belin Shugaban Kungiyar Kwadagon Najeriya Joe Ajaero

Ajaero NLC

Hukumar tsaron farin kaya ta DSS ta bada belin shugaban kungiyar kwadago na Najeriya, NLC, Joe Ajaero bayan Kama shi da tayi a safiyar litinin.

Alfijir Labarai ta rawaito wani mai rajin kawo cigaban jama’a kuma tsohon dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar AAC, Omoyele Sowore ne ya bayyana hakan a wani sako da ya wallafa a shafin sa na X a daren Litinin.

An kama Ajaero a safiyar ranar Litinin a filin jirgin sama na Nnamdi Azikwe dake Abuja, a akan hanyar sa ta zuwa kasar Ingila domin gudanar da wani aiki a hukumance.

Ajaero dai zai halarci taron kungiyar ‘yan kwadago da za a yi a Landan, wanda za a fara a litinin dinnan.

Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *