Dubun Wani Soja Da Ke Sayar Wa ’Yan Ta’adda Bindiga Ta Cika A Birnin Tarayya Abuja

Alfijr ta rawaito wani soja a birnin tarayya Abuja, ya shiga hannun hukumar DSS kan zarginsa da sayar da bindiga ga masu garkuwa da mutane.

Alfijr Labarai

Wani mai leken asiri ya shaidawa ofishin DSS da ke Gwagwalada, nan take suka yi hadin guiwa da jami’an tsaron Zuba, wajen kamo wanda ake zargin.

Majiyar ta ce, “An gano wanda ake zargin a baya ma ya taba sayar musu da bindigar kan N300,000.

“Sai na biyu kuma da ya sayar kan N200,00, wanda ’yan Bindigar suka biya, amma ya gaza kawo musu,” a cewar majiyar tamu.

Haka kuma majiyar ta ci gaba da cewa, bayan da DSS din suka samu nasarar kamo masu satar mutanen, sun sanar da su batun.

Alfijr Labarai

Bada bata lokaci ba aka shirya sintiri na musamman domin kama shi da kuma tabbatar da gaskiyar lamarin.

Nan take suka shirya dabara aka tuntube shi a matsayin masu satar mutane ne ke son sayen wata bindigar kirar AK-47, kan Naira miliyan uku.

Babu bata lokaci ya bayyana inda za mu hadu mu karba, muka amince, yana zuwa da bindigar kuwa aka kama shi.

Alfijr Labarai

Bindigar cike take da harsasai kuma a motarsa ma an samu wasu albarusan guda 30.

Daga nan muka kai shi ofishinmu, sannan muka mika shi ga DSS din, inji majiyar.

Rundunar Sojoji daga shalkwatasu ta Abuja, sun je ofishin Jami’an Tsaron sa kan da ke Zuban, in da suka dauki bayaninsu kan lamarin a rubuce.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Aminiya

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *