Karfin Hali! Ya Sace Wayar Dan Sanda A Caji Ofis Lokacin Bayan Ya Je Neman Belin Abokinsa

Alfijr ta rawaito wani abin mamaki lokacin da aka gurfanar da wani mutum mai shekara 45, a gaban kotu bisa zarginsa da satar wayar dan sanda da darajarta ta kai Naira 120,000.

Alfijr Labarai

An dai gurfanar da ɓarawo a gaban kotun Majistare da ke Ogba a jihar Lagos ranar Juma’a.

’Yan sanda sun ce lamarin ya faru ne lokacin da wanda ake zargin ya je caji ofis dinsu da ke Bolade, domin yin belin abokinsa da aka tsare.

Dan sanda mai gabatar da kara, Rachael Williams, ya ce wanda ake zargin ya shiga ofishin ne lokacin da wayar ke ajiye a kan tebur nan take ya kundume wayar abinsa.

Alfijr Labarai

Koda aka waiwayi wanda ake zargin musanta zargin satar wayar, amma ’yan sanda duk da haka sun gurfanar da shi kan zarge-zargen sata da shiga ofishin ba bisa ka’ida ba.

Rachael ya ce, gano satar wayar ya jefa ’yan sandan da ke bakin aiki cikin rudani, inda nan take D P O din wajen ya ba da umarnin gudanar da binciken kan yadda aka haihu a ragaya.

Mai Shari’a O.O. Akingbesote, ya bayar da wanda ake zargin beli a kan Naira 100,000 da kuma mutum biyu da za su tsaya masa.

Daga nan ne alkalin ya dage ci gaba da sauraron karar tare da ba da umarnin tsare wanda ake zargin a gidan gyaran hali na Ƙirkiri kafin cikar sharudan belin

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *