Dubun Wani Tsohon Ɗan Ƙwallon Ƙafa Ta Cika A Najeriya Kan Safarar Hodar Iblis-NDLEA

Alfijr ta rawaito hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA ta kama wani tsohon dan ƙwallon kafa, Emmanuel Okafor a filin jirgin saman Murtala Muhammed dake Ikeja, bisa laifin safarar hodar iblis.

Alfijr Labarai

Mai magana da yawun hukumar ta NDLEA, Femi Babafemi ne ya bayyana hakan a ranar Lahadi a Abuja.

Ya bayyana cewar, an kama Okafor ne a lokacin da ya taso daga Sao Paulo, Brazil ta birnin Addis Ababa, ya kuma taso ne a cikin jirgin Ethiopian Airlines.

Kakakin ya bayyana cewa wanda ake zargin yana ɗauke da hodar iblis mai nauyin kilogiram 1.4 da aka boye a hannun jakunkunansa da kuma a saman jakunkunan.

Ya kara da cewa an kama matashin ne ɗan shekaru 33 dan asalin karamar hukumar Arochukwu da ke jihar Abia ne a ranar 26 ga watan Satumba, bayan jami’an hukumar suka bankado inda ya boye haramatattun kayan .

Alfijr Labarai

Da ake masa tambayoyi Okafor ya ce shi dan kwallon kafa ne a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Najeriya, Enugu FC, inda ya yi wasa har tsawon shekaru hudu kafin ya tafi Sri Lanka a shekarar 2014.

“Ya ce ya koma Brazil daga Sri Lanka bayan ya yi wasa na kaka biyu, amma bai iya ci gaba da buga kwallon kafa a Brazil ba saboda ba shi da takardu,” in ji Babafemi

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *