EFCC ta saka Mele Kyari a jerin wadanda ta ke fako yayin da kotu ta rufe asusun sa na banki

FB IMG 1755695257366

Hukumar EFCC ta sanya tsohon shugaban kamfanin man fetur na kasa (NNPCL), Mele Kyari, cikin jerin wadanda take sa ido a kansu saboda bincike kan kudaden gyaran matatun mai da suka kai dala biliyan 7.2.

A jiya Talata, Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta bayar da umarnin rufe wasu asusun banki guda hudu da aka alakanta da Kyari na tsawon kwanaki 30, bisa zargin hada baki, amfani da ofishi ba bisa ka’ida ba, da kuma almundahanar kudi.

Jaridar Daily Trust ta rawaito EFCC ta ce binciken ya kai gaba, inda aka kama kuma aka yi wa abokan aikin Kyari tambayoyi, tare da gano sama da naira miliyan 661 da ake zargin sun shiga asusun sa ta hanyar da ba ta dace ba.

Kotun ta dage shari’ar zuwa 23 ga Satumba 2025 domin samun karin rahoton ci gaban bincike daga hukumar.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *