Gwamnatin Najeriya ta rage farashin wankin ƙoda daga Naira dubu 50 zuwa dubu 12 a asibitocin gwamnati

FB IMG 1742320893164

Gwamnatin Tarayya ta sanar da sabon tsarin tallafi domin rage farashin kuɗin wankin koda ga masu cutar koda a asibitocin tarayya da ke fadin kasar nan.

A karkashin wannan sabon tsari, marasa lafiya za su rika biyan Naira 12,000 kacal a kowanne wankin koda maimakon tsohon kudin da ya kai Naira 50,000.

A wata sanarwa da mataimakin daraktan yaɗa labarai, Alaba Balogun, Ma’aikatar Lafiya da Walwalar Jama’a ta bayyana cewa wannan mataki na daga cikin shirye-shiryen gwamnatin Shugaba Tinubu na rage radadin kudi da kuma bunkasa damar samun kulawar lafiya ga ‘yan kasa, musamman masu rauni.

An fara aiwatar da shirin a asibitoci 11 na tarayya da ke cikin manyan yankunan siyasa na kasar nan, wadanda suka hada da:

Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano

Asibitin Koyarwa na Jami’ar Maiduguri

Asibitin Koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa, Bauchi

Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jos

Babban Asibitin Kasa, Abuja

Cibiyar Lafiya ta Tarayya, Ebute Metta

Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ibadan

Asibitin Koyarwa na Jami’ar Benin

Cibiyar Lafiya ta Tarayya, Yenagoa

Asibitin Koyarwa na Tarayya, Owerri

Cibiyar Lafiya ta Tarayya, Abakaliki

Ma’aikatar ta karyata rahotannin da ke cewa an ware yankin Arewa maso Yamma daga shirin, inda ta jaddada cewa dukkan yankuna sun samu shiga.

“Gwamnatin Tarayya ba ta ware jihohin Arewa maso Yamma daga tallafin jinyar koda ba, sabanin yadda wasu rahotanni suka yi ikirari,” in ji Alaba Balogun, Mataimakin Darakta kuma Shugaban Sashen yaɗa labarai da Hulda da Jama’a na ma’aikatar.

Ya kara da cewa za a ci gaba da fadada shirin zuwa wasu asibitoci na tarayya domin kara yawan jama’a da za su iya amfana.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *