Ƙasa da kwanaki bakwai bayan saukarsa daga Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello zai gurfana gaban kotu, kan tuhuma da zargin karkatar da Naira biliyan 80 daga aljihun gwamnati zuwa aljihun sa.
Alfijir labarai ta rawaito hukumar EFCC ba ta gabatar wa kotu wasu sabbin tuhume-tuhume a kan Bello ba, sai kawai ta yi kwaskwarima kan cajin tuhume-tuhumen da kotu ke wa, ɗan uwan tsohon gwamnan da makusancinsa, waɗanda kotu ke tuhuma kan zargin karkatar da biliyoyin nairorin Jihar Kogi.
Abin da kawai EFCC ta yi shi ne ɗora tuhume-tuhumen da ake wa Yahaya Bello a cikin waccan shari’a da ke gaban kotu.
A shari’ar dai ana tuhumar ƙanen Yahaya Bello mai suna Ali Bello da wani mutum mai suna Dauda Suleiman da laifin karkatar da kuɗaɗe.
To amma a cikin shari’ar yanzu an haɗa da Yahaya Bello, wanda shi kuma aka tuhume shi da zargin karkatar da Naira biliyan 80 zuwa aljihun sa, adadin kuɗaɗen da EFCC ke nema a hannunsa sun kai N80,246,470,089.88.
Tuhume-tuhumen sun nuna cewa abokin harkallar kuɗaɗen mai suna Abdulsalami Hud, wanda Jami’in Kula da Harkokin Kuɗaɗe ne na gidan Gwamnatin Jihar Kogi, ya cika wandon sa da iska.
To sai dai kuma tuni har sabuwar Gwamnatin Jihar Kogi ta yi wa EFCC zazzafan raddin cewa hauragiya ta ke yi, domin laifukan da ake cajin Yahaya Bello da aikatawa, ta ce an yi su ne tun wajen Satumba, 2015, lokacin Yahaya Bello bai ma zama gwamna ba.
Kwamishinan Yaɗa Labaran Jihar Kogi, Kingsley Fanwo, wanda kuma shi ne dai kwamishinan yaɗa labarai a mulkin Yahaya Bello, shi ne ya fito da bayanin da ke ƙunshe da raddin da gwamnatin ta Jihar Kogi ta yi wa EFCC.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H3iC9eVfJI012LJzvCQn5V