Wata Sabuwar! An Taso Da Maganar Dawo Da Sanusi Matsayin Sarkin Kano A Gaban Majalisa

IMG 20240207 115029

Wata kungiya mai suna “Yan Dangwalen Jihar Kano” ta rubutawa majalisar dokokin jihar Kano takardar neman rusa dokar kafa karin masarautu hudu da suka hadar da Gaya, Rano, Karaye da Bichi, wadanda gwamnatin da ta shude ta kafa, sannan sun nemi a maido da tsohon Sarkin Kano Sanusi II.

Alfijir labarai ta rawaito a wata wasika mai kwanan watan Fabrairu 5, 2024 da Wata kungiya ta aike wa kakakin majalisar dokokin jihar Kano, ta ce rusa masarautu tare da maido da Sanusi a matsayin sarkin Kano “zai samar da hadin kai, zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar Kano”.

Wasikar tana cewa:

“Mun rubuto wasikar ne don rokon a wannan majalisa data yi gyara a dokar masarautun jihar kano, muna so a gyara dokar ta yadda za’a rushe sabbin masarautun da aka kirkira guda hudu.

“Mun yi imanin idan har aka hade masarautun suka koma masarauta daya za a fi samun hadin kai da cigaban al’ummar Kano. Rushe masarautun zai inganta zaman lafiya da tattalin arzikin jihar kano, don haka muke neman Wannan gida zai yi abun daya dace daidai da doka.

Mun amince da ikon da Majalisar Dokokin Jihar Kano ke da shi kan harkokin tafiyar da masarautu.

“Duk da haka, cikin kaskantar da kai muna rokon majalissa da ta sake duba matakin tsige Sarki Sanusi Lamido Sanusi daga karagar mulki. Imaninmu ya ta’allaka ne a kan cewa mayar da shi kan karagar mulki za ta samar da hadin kai, zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar Kano .”

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H3iC9eVfJI012LJzvCQn5V

One Reply to “Wata Sabuwar! An Taso Da Maganar Dawo Da Sanusi Matsayin Sarkin Kano A Gaban Majalisa”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *