Fadar Shugaban Ƙasa ta yi kira da a ɗauki matakin shari’a kan fitaccen ɗan soshiyal midiya, Martins Vincent Otse, wanda aka fi sani da VeryDarkMan (VDM), bisa wani sautin murya da ake dangantawa da Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Mai bai wa Shugaban Ƙasa shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai, Bayo Onanuga ne, ya yi kiran inda ya zargi VDM da yaɗa bayanan ƙarya a kan Tinubu .
Onanuga, na wannan zargi ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Laraba, yayin da yake mayar da martani kan ce-ce-ku-ce da ake yi kan wani sautin muryar da ake zargin na Shugaban Ƙasar ne.
A cikin sautin muryar da ake dangantawa da shugaban, an jiyo yadda ake bayani a kan yadda Tinubu ya ci zaɓe da kuma dalilin da ya sa gwamnatin Najeriya ke ci gaba da ciyo bashi.
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t