Rundunar yan sanda ta kasa reshen jihar Kano ta ce ta dakatar da yin hawan sallah ga dukkanin masarautun Kano dake karkashin Sarki Aminu Ado Bayero da Sarki Sanusi II.
Hakan na kunshe ne cikin wata wasiƙa mai dauke da sa hannun mataimakin kwamishinan Yan sandan Kano mai kula da aiyukan Rundunar DCP Lawan Isa Mani wadda aka turawa Sakataren Sarki Aminu, wato Abdullahi Kwaru, mai dauke da kwanan watan 27 ga watan mayu 2026.
Wasikar ta ce an hana yin dukkanin hawan ne saboda tabbatar da zaman lafiyar jihar Kano.
Idan za a iya tunawa Dukkanin Sarakunan Kano Sarki Aminu Ado Bayero da Sarki Muhammadu Sanusi II sun yi shirin gudanar da hawan Daushe duk a wannan ranar, wanda hakan ya sanya fargaba a zukatan al’ummar jihar Kano baki daya.
Don haka rundunar ta ɗauki wannan matakin domin kawo zaman lafiya a jihar.
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t