Rana Dubu! Dubun Wani Mai Garkuwa Ta Cika Bayan Yaje Karɓar Kuɗin Fansa

Screenshot 20240402 211801 com.android.chrome edit 2518018284509

Yan sandan jihar Adamawa sun kama wani da ake zargin mai garkuwa da mutane ne mai suna Roland Raymond.

Alfijir labarai ta rawaito kakakin rundunar yan sandan jahar SP Sulaiman Yahya nguroje, ya ce rundunar ta cafke Mista Raymond ne a ƙauyen Detti da ke Ƙaramar hukumar Ganye ta jihar.

Yace an sami Nasarar kama Raymond mai shekaru 32 a lokacin da yake ƙoƙarin karɓar kuɗin Fansa, tare da haɗin gwiwar mafarautan jihar.

Sanarwar ta ce, “Rundunar ‘yan sandan Jihar Adamawa ta kama wani Roland Raymond mai shekara 32 da haihuwa, mazaunin ƙauyen Detti, ƙaramar hukumar Ganye, bisa laifin cin zarafi mai alaƙa da garkuwa da mutane.

“An kama wanda ake zargin ne biyo bayan rahoton wasu mutane —Alhaji Yahaya Kongo da Abraham Paul — waɗanda suka bayyana cewa wanda ake zargin ya kira su ta wayar tarho ya buƙaci su biya Naira dubu 600 a matsayin kuɗin fansa.

“Bayan samun ƙorafin ne ‘yan sandan da ke yankin Ganye, tare da haɗin gwiwar mafarauta, suka yi gaggawar tattara bayanai tare da cafke wanda ake zargin a wajen karɓar kuɗin.

SP Sulaiman ya kara da cewar, “Za a gurfanar da wanda ake zargin zuwa kotu bayan  kammala bincike.”

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/CJ2q8cmhhOxFY6OEgwV5vk

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *