Fashi Barnar Aiki: Sabuwar Hukumar Tara Haraji ta Ƙasa Ta Fara Aiki

IMG 121214 01126 1767265950186

Sabuwar Hukumar Haraji ta Ƙasa, Nigeria Revenue Service (NRS), ta fara aiki a hukumance a wannan rana ta farko a sabuwar shekara ta 2026, inda ta maye gurbin tsohuwar hukumar karbar haraji ta kasa (FIRS) a matsayin babban hukuma ta karɓar haraji a ƙasa.

Sauyin ya biyo bayan rattaba hannu da Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya yi kan Dokar Kafa Hukumar NRS ta 2025 a watan Yuni.

An ƙaddamar da fara aikin ne a Abuja, inda aka bayyana sabon tambari (logo) da tsarin alamar hukumar.

Da yake jawabi kan ci gaban, Shugaban Hukumar NRS, Zacch Adedeji, ya bayyana sauyin suna da tsari a matsayin wani muhimmin ci gaba a ƙoƙarin da ake yi na zamanantar da tsarin tara haraji a Najeriya.

A cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara kan harkokin yaɗa labarai, Dare Adekanmbi, ya fitar, Adedeji ya ce sabon tsarin hukuma da alama suna nuna sabon ƙuduri na gina hukuma guda ɗaya, mai inganci kuma mai bai wa jama’a hidima, wadda ta yi daidai da ajandar sauyin tattalin arziƙin ƙasa.

Ya bayyana cewa kafa NRS na nuni da ci gaba da manufa ɗaya, ƙara ƙarfin aiki, da hangen nesa na gaba domin tallafa wa masu biyan haraji da ƙarfafa ci gaban ƙasa.

Adedeji ya kuma jaddada cewa hukumar za ta himmatu wajen gaskiya, haɗin gwiwa, da ingantacciyar hidima, tare da gina amincewar jama’a da samar da ci gaba na bai ɗaya a faɗin Najeriya.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *