Fassarar Wasu Muhimman Bayanai  Daga Cikin Jawabin Ranar Samun Yancin Kai Na Shugaba Tinubu

IMG 20241001 075814 863

Shugaba kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi jawabi ga ‘yan Nijeriya a wani ɓangare na bikin ranar 1 ga Oktoba ta samun ‘yancin kan ƙasa, inda a yanzu aka cika shekaru 64 da Turawan mulkin-mallaka na Biryaniya suka miƙa wa Nijeriya mulkin kanta.

Gwamnati Na Yin Iya Ƙoƙarinta Don Inganta Rayuwar ‘Yan Najeriya

Bikin na 1 ga Oktoba na wannan shekarar na zuwa a lokacin da ‘yan Najeriya ke fama da matsalolin tattalin arziki inda rayuwa ta yi tsada kuma suke kokawa ga gwamnati kan ta kawo gyara.

Shugaba Tinubu ya ce sun san halin da jama’a ke ciki, sun ji koken ‘yan Najeriya na tsadar rayuwa da wahalar samun ayyukan yi masu kyau, kuma gwamnati na ayyuka don magance waɗannan ƙalubale.

“A matsayina na shugaban ƙasarku, ina tabbatar muku cewa mun duƙufa wajen neman mafita ta dindindin don kawar da wahalar da ‘yan ƙasarmu ke sha,” in ji Shugaba Tinubu, yayin da ya sake kira ga ‘yan Najeriya da su yi haƙuri saboda irin sauye-sauyen da gwamnatinsa ke yi sun fara kawo ci gaba.

Kakanninmu Sun Assasa Tushen Gina Ƙasa Jagora A Afirka

A jawabin nasa, shugaban na Nijeriya ya yabi ‘yan ƙasa da suka yi gwagwarmayar ƙwatar ‘yancin kai tare da zaɓar tsarin dimokuraɗiyya a matsayin salon jagoranci, wadda za ta zama abar koyi ga sauran ƙasashen Afirka.

Ya ce Najeriya da aka kafa na da manufar jagorantar sauran ƙasashen Afirka wajen fitar da al’uma daga ƙangin talauci, jahilci da koma-baya, ƙasar da kowanne ɗan Afirka zai dinga alfahari da koyi da ita.

Tinubu ya ci gaba cewa “Bayan shekaru sama da 60, idan muka waiwaya, ‘yan Najeriya a ko’ina suke a ban-ƙasa za su ga yadda muka samu nasara wajen cika burin kakanninmu.”

Haɗin Kai Abin Koyi Ga Sauran Ƙasashen Duniya

Shugaba Tinubu ya kuma ce duniya na shaida wa tare da amfana da akidar fada-a-cika ta ‘yan Najeriya, inda suke da kwarewa a bangarorin kaifin kwakwalwa, kwarewa a fannin sana’o’i, kimiyya, fasahar kere-kere da gina kasa, wanda su ne irin burin da aka kafa kasar a kai, kuma suna ci gaba da ayyuka don ganin kasar ta ci gaba.

Tinubu ya ce a yayinda ake kokarin mayar da hankali kan yin abubuwan da ba a yi ba da inda aka yi kuskure a matsayin kasa, dole ne mu kalla tare da yaba yadda muka zauna a matsayin kasa daya dunkulallaiya duk da kalubalen da ake fuskanta.

“Tun bayan samun ‘yancin kai, Najeriya ta tsira daga rikice-rikice da hayaniya da dama da suka rusa da karya wasu kasashen duniya da dama. Shekaru shiba bayan samun ‘yancin kai, kasar ta fada rikicin siyasa da ya jefa ta yakin basasa. Tun bayan fita daga kangin duhun wancan lokacin, mun koyi rungumar bambance-bambancen da ke tsakaninmu tare da ci gaba da rayuwa mai hadin kai sosai,” in ji shugaban na Najeriya Tinubu.

Ya ce “Duk da kalubale da dama da kasarmu ke fuskanta, amma mun zama masu karfi, hadin kai da kasancewa kasar mai cikakken ikon mulkin kanta.”

Kowa Ya Jajirce Don Gina Najeriya

Shugaba Tinubu ya kuma bukaci ‘yan Nijeriya da su jajirce tare da sake zage damtse don ganin kasar ta ginu yadda ya kamata.

Ya ci gaba da cewa Najeriya da ake bukatar gina wa ita ce wadda za ta amfanin ‘yan kasar a yau da kuma gobe, yana mai kira da a yi waiwaye don kar a sake maimaita kura-kuran da aka yi a baya.

“A yayinda muke bikin murnar irin cigaban da muka samu a shekaru 64 da suka gabata, dole ne kuma mu yi duba ga irin damarmakin da muka rasa, da kura-kuran da muka aikatama baya. Idan muna son zama kasa mafi girma a duniya, kamar yadda Ubangiji ya kaddara mana, to dole ne kar mu bar kura-kuranmu su biyo mu a rayuwarmu ta nan gaba,” Tinubu ya fada wa ‘yan Najeriya.

“Zabi Tsakanin Gyara Ko Ci Gaba Da Durƙushewa”

Wata matsala da ke ci wa ‘yan Nijeriya tuwo a kwarya a yau ita ce matsalar tsaro, musamman ma a arewa maso-yammacin ƙasar da ake fama da hare-haren ‘yan bindiga da karkuwa da mutane don neman fansa, sai arewa maso-gaba da ke fama da rikicin ‘yan ta’adda da ke iƙirarin jihadi.

A yankin kudu maso-gabashin Nijeriya ana fama da rikicin ‘yan a-ware, yayin da yankin kudu-maso kudu kuma ke fama da rikicin ɓarayin mai da fasa bututu wanda ke shafar yawan albarkatun mai da Najeriya ke fitarwa. Yankunan kudu maso-yamma da arewa ta tsakiyar Nijeriya kuma na fuskantar rikicin manoma da makiyaya.

Da yake bayanin yadda gwamnatinsa ke ƙoƙarin shawo kan wannan matsalar, shugaba Tinubu ya ce ya karɓi gwamnati watanni 16 da suka gabata a wata gaɓa mai matuƙar wahala.

Ya ce “Tattalin arziki ya shiga halin ni-‘ya-su, al’amuran tsaronmu sun gama taɓarɓarewa. Mun tsinci kawunanmu a hanya mai wahala, wadda zaɓin da ya rage mana shi ne ko dai mu kawo gyara ko mu ci gaba da bin hanyar durƙushewa. Mun zaɓi gyara tattalin arziki, siyasa da fasalin tsaronmu.”

Shugaba Tinibu ya shaida wa ‘yan Najeriya cewa gwamnatinsa na samun nasarar yaƙi da ta’addanci da hare-haren ‘yan bindiga.

Ya ce “Manufarmu ita ce mu kawar da dukkan barazanar ‘yan Boko Haram, masu garkuwa da mutane don neman fansa, ‘yan bindiga da duk wani nau’i na tsaurin ra’ayi. A cikin shekara guda, gwamnatinmu ta kassara kwamandojin ‘yan ta’addar Boko Haram da masu garkuwa sama da kowanne lokaci a ƙasar.”

Tinubu ya ƙara da cewar tun bayan hawansa mulki sojojin ƙasar sun kashe kwamandojojin Boko Haram da ‘yan bindiga sama da 300 a yankunan arewa maso-gabas da arewa maso-yammacin ƙasar.

1. “Saboda sauye-sauyen da aka yi, kasarmu ta samu masu zuba hannun jari daga kasashen waje, wanda ya kai sama da dala biliyan 30.”

2. “Mun gaji sama da dala biliyan $33 cikin watanni 16.

3. “Mun biya bashin dala biliyan 7 da aka gada

4. “Mun share hanyoyin da ake bi bashi na sama da Naira tiriliyan 30

5. “Mun rage yawan bashi kaso 97% zuwa 68%”

6. “Mun yi nasarar ajiye rar kudi da ya kai Dala biliyan $37

7. “Mun samu nasarar kawar da mayakan Boko Haram sama da 300 a cikin shekara guda.”

8. “Mun amince da Asusun Ba daAgajin Bala’i don tara kudade masu zaman kansu da na jama’a don taimakawa alummar Najeriya cikin gaggawa

9. Gwamnatin Shugaba Tinubu ta ba da umarnin a gudanar da gwajin gaskiya a duk madatsun ruwa na kasar nan domin kaucewa bala’i a nan gaba.

10. Gwamnatin tarayya a shirye take ta taimakawa jahohi talatin da shida da har da Abuja FCT wajen siyan motocin CNG don zirga zirgar jama’a cikin rahusa.

11. “Mun yi farin ciki da aiwatar da Asusun Lamuni na Ilimin Najeriya (NELFUND)”

12. Nan ba da jimawa ba gwamnati za ta bayyana duk wadanda suka ci gajiyar karramawar kasa a 2024

13. Gwamnati za ta kira taron matasa na kasa na tsawon kwanaki 30 don magance batutuwan da suka shafi ilimi, aikin yi, da tsaro.

A ranar 1 ga Oktoban kowacce shekara Najeriya ke bikin murnar samun ‘yancin kai daga Turawan mulkin-mallaka na Birtaniya, inda a bana take cika shekaru 64 da samun ‘yancin kai.

Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *