FCCPC tace Barazanar Ficewa daga Najeriya ba zai hana mu hukunta shi ba

FB IMG 1746386326875

Hukumar da ke sanya ido kan farashi da kare haƙƙin masu sayen kaya ta Najeriya (FCCPC), ta ce barazanar da kamfanin Meta ya yi na ficewa daga ƙasar, ba zai hana a hukunta shi ba.

BBC Hausa ta rawaito cewa Hukumar ta ce ba za a janye shari’ar da ake yi da Meta ba duk da barazanar da ya yi.

FCCPC ta ce kamfanin ya yi barazanar ficewa daga Najeriya ne domin a ji tausayinsa, da kuma matsawa hukumar canza matakin da ya ɗauka na cin tarar kamfanin.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da daractan hukumar, Ondaje Ijagwu ya fitar ranar Asabar.

Hakan kuma na zuwa ne bayan wani gargaɗi da Meta ya yi da farko cewa “za a tilasta masa rufe shafukan Facebook da Instagram a Najeriya don kauce wa barazanar fuskantar hukunci”.

Hukumar ta zargi Meta da yi wa bayanan ƴan ƙasar kutse, ciki har da aika bayanan ba tare da izininsu ba da rashin mutunta masu amfani da shafukan kamar yadda ake yi a sauran ƙasashe da kuma ɓullo da tsare-tsare da ba su da kyau kan ƴan ƙasar.

A bara ne hukumomin sanya ido uku na Najeriya suka lafta wa kamfanin tarar da ta kai fiye da dala miliyan 290, bisa zargin kamfanin da karya wasu dokoki.

Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news ku shiga nan  👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/KoLt2IMlnQfJPP6zNrcNKD

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *