Gwamnatin Kano ta ware miliyan dubu 4, da miliyan dari 8, domin bawa kansiloli damar gudanar da ayyukan raya kasa a mazabinsu.

FB IMG 1746440014572

Gwamna Abba ne ya bayyana haka yayin taro na musamman da kansilolin jihar Kano 484  a dakin taro na Coronation dake gidan gwamnati.

Gwamnan  wanda ya bukaci zababbun kansilolin su lalubo ayyukan da alumarsu na kasa suka fi bukata musamman a bangaren ilimi da samar da ruwan sha da gina bandakuna, yace gwamnati tayi wannan tsari ne domin tabbatar da ayyukan raya kasa sun shiga lungu da sako na jihar Kano.

Yace gwamnati ta ware kudin a karkashin ma’aikatar kananan hukumomi Wanda da zarar kowane kansila ya bujuro da aikin gwamnati zata sahhale masa domin fara aiwatarwa.

Yace da zarar kansilolin sun aiwatar da ayyukan da ake bukata, gwamnatinsa a shirye take ta sake basu wasu makudan kudaden domin aiwatar da wasu ayyukan na cigaban aluma.

Ya bukaci zababbun kansilolin, da su zamo masu biyayya ga shugabanninsu tare da yin aiki tare bisa gaskiya da rikon amana.

Ya ce gwamnati zata ci gaba da basu dama wajen lalubo matan  da zu amfana da tallafin da gwamnatinsa take bayarwa a kowane karshen wata kasancewar sune suka fi kusaci da al’uma.

Kazalika gwamna Abba Kabir Yusuf ya Kara da cewa suma nadaddun kansiloli, gwamnatinsa bazata barsu a baya ba,  zata samar da hanyoyin da za’a tallafa musu.

Daga nan ya gargadi masu taba muhibbar Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da cewa suna yin hakan ne domin bata masa suna, tare da cewa suna da yankinin Sanata Rabiu Musa Kwankwaso duk ya fisu nagarta.

A baya bayan nan ne dai majalisar zartaswar jihar Kano ta ware sama da naira biliyan 15 domin biyan tsoffin kansilolin da suka yi aiki a gwamnatin tsohon gwamnan Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje daga shekarar 2014-2024 hakkokinsu da gwamnatin baya ta gaza biyansu.

Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news ku shiga nan  👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/KoLt2IMlnQfJPP6zNrcNKD

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *