Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya yi wa tsohon Sakataren Gwamnatin Kano, Baffa Bichi martani bisa zarge-zargen da ya fada akan gwamnatin.
A wata hira da manema labarai da ta karade kafafen watsa labarai, an jiyo Baffa Bichi, wanda aka cire shi daga muÆ™amin sakataren gwamnatin, na cewa an É—auki matakin ne don ya ki amincewa da ya sahale a rika diban Naira biliyan 2 duk wata ana saka wa a asusun Rabi’u Musa Kwankwaso, jagoran Kwankwasiyya.
A wani taro da kansilolin mazaÉ“u 484 na jihar a yau Lahadi, gwamna Abba ya ce maganganun da Bichi ya yi “babu hankali da lissafi da aiki da Æ™waÆ™walwa a wannan maganar.”
A cewar gwamna Abba, babu hankali a ce gwamnatin sa da ko shekaru biyu bata cika ba amma har a rika cewa ta kwashe dukiyar jihar sama da ta gwamnatin da ta gabata.
Ya ce an baiwa Bichi mukami mai girma amma ya fito ya na wasu malamai ma kazafi da babu hankali a ciki, inda ya ce ya binciki kan sa tare da duba akan dalilin da ya sa aka cire shi.
Ya kuma gargaÉ—i Bichi da ya daina taba Kwankwaso domin shi shugaba ne adali da ya yi mulkin jihar cikin tsafta ba tare da din hanci ba.
Ya kara da cewa Kwankwaso shugaba ne kuma hakkin ne a kan gwamnatin sa ta kare mutuncin da martabar sa da ma sauran manyan jihar, inda ya ja kunnen Æ´an siyasa akan taba muhibbar shugabanni.
Hakazalika gwamnan ya kuma yi gargaÉ—i ga gidajen rediyo da su guji yada irin waÉ—annan kalamai, inda ya kara da cewa gwamnatin sa ba za ta amince da hakan ba.
Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news ku shiga nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/KoLt2IMlnQfJPP6zNrcNKD