Gobara Daga Kogi! Bankin Polaris Ya Tasamma Yaki Da Musulunci Da Musulmai

Alfijr ta rawaito shugaban wani sashi na bankin Polaris ta tura wa da ma’aikatan bankin musulmai da wata wasika mai dauke da umarnin hana su zuwa sallar juma’a.

Alfijr Labarai

Wasikar da shugaban wani sashi na bankin Damilola Adebara, ta aikawa da ma’aikatan bankin musulmai ta ce bankin ba shi da tsarin barin ma’aikata su tafi ibada a lokacin aiki domin hakan na shafan bankin kai tsaye.

Saboda haka kada wani ma’aikacin bankin musulmi ya kara tafiya Sallar juma’a. In Ji ta.

Wasikar ta sake cewa: “An lura cewa a ranar Juma’a, kuna barin aikinku ku tafi sallar Juma’a duk da sani abin da rashin ku zai janyo ga aiki a Cibiyar Yes.

Ku sani cewa babu wani wuri a tsarin aikin bankin da ya bawa ma’aikata damar tafiya ibada a lokacin aiki.

Alfijr Labarai

Daga yanzu ba za a rika amincewa da haka ba a Cibiyar Yes, kuma duk wanda ya saba zai fuskanci hukunci.

Ana sa ran kowa ya amsa cewa ya ga wannan sakon. Na gode.

Sakon na imel ya nuna cewa ma’aikatan na aiki ne a sashin Cibiyar YES, wani bangare na bankin.

Sai dai mu kuma muna kira ga duk wani Musulmi dake amfani da asusun bankin Polaris daya gaggauta janye kudin shi daga cikin bankin domin nuna kishin shi ga addinin musulilci da musulmai.

Alfijr Labarai

Muna rokon ubangiji Allah ya daukaka addinin musulilci da musulmai.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

2 Replies to “Gobara Daga Kogi! Bankin Polaris Ya Tasamma Yaki Da Musulunci Da Musulmai

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *