Gobara Ta Lalata Dukiya Ta N20m, Ta Kuma Lakume Rayukan mutane 15 A Kano

Alfijr ta rawaito hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta bayyana cewar mutane akalla 15 ne suka rasa rayukansu tare da samun asarar dukiya da ta kai ta Naira miliyan 20 a gobara daban-daban da ta tashi a faɗin jihar a cikin watan Oktoban da ya gabata.

kakakin hukumar kashe gobara ta jihar Kano, Saminu Yusuf Abdullahi ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis a Kano.

Abdullahi ya ce hukumar ta kuma kokari inda ta ceto rayukan mutane 25 da kuma dukiyoyin da kudinsu ya kai kimanin Naira miliyan 43.3 daga gobara 35 da aka samu a lokacin.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *