Rundunar Yan Sanda Ta Kashe Masu Garkuwa 4, Da Kama Wata Mata Mai Yi Wa ‘Yan Bindiga Safarar Makamai

Alfijr ta rawaito rundinar ‘yan sandan jihar Kaduna ta samu nasaran kashe wasu miyagun ‘yan ta’adda 4, wadanda suka addabi al umma da garkuwa da mutane a jihar

Kakakin ‘yan sandan jihar Kaduna DSP Muhammad Jalige ya shaida wa manema labarai cewa sun jima suna yiwa ‘yan ta’addan, tarko, kuma sun sami nasarar taresu a akan hanyar Saminaka zuwa Jos suna tafiya a cikin mota kirar Sharon blue, direban motar mai suna James Dawi, dan shekara 31 wanda ya fito daga garin Vom karamar hukumar Jos South jihar Plateau.

Alfijr

Jalige yace Lokacin da ‘yan ta’addan suka ankara ‘yan sanda na bin su akan hanyar Saminaka zuwa Jos, sai suka bude wa ‘yan sandan wuta, a gurin musayen wuta na tsawon mintuna 30 ‘yan sanda suka samu nasaran aika ‘yan ta’addan zuwa lahira.

Bayan ‘yan sanda sun duba motar ‘yan ta’addan, sun samu bindigogi kirar AK47 da harsashi guda 140.

Alfijr

‘Yan sanda sun kuma kama wata bafulata, wacce ta ke safaran bindigogi da harsashi zuwa ga ‘yan ta’addan jeji a cikin jihar Kaduna.

Kakakin rundunar D S P Muhammad Jalige ya kara kira ga Al ummar jihar Kaduna dasu sanar wa rundunar duk wani motsi da suka gani wanda basu gamsu da shi ba.

Slide Up
x