Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayyana cewa zabi Murtala Sule Garo a matsayin Mataimakin Gwamna ne saboda kwarewarsa da kuma jajircewarsa wajen ci gaban jihar Kano.
Gwamnan ya ce gwamnatin sa ta yi nazari sosai domin zakulo mutumin da zai iya bayar da gudunmawa mai ma’ana ga cigaban jihar.
Ya bayyana hakan ne yayin bude taron majalisar zartarwa karo na 39 da aka gudanar a Fadar Gwamnatin Kano ranar Talata.
A wata sanarwa da Babban Sakataren Yada Labaran Gwamnan Kano, Mustapha Muhammad, ya aikewa manema labarai ya ce Gwamna Yusuf ya aike da sunan Garo zuwa Majalisar Dokokin Jihar Kano ne bayan murabus din tsohon Mataimakin Gwamna, Comrade Aminu Abdulsalam Gwarzo.
Gwamnan ya ce mutane da dama sun nemi matsayin, amma sai da aka duba tarihinsu, ayyukansu da kuma irin gudunmawar da za su iya bayarwa yanzu da nan gaba.
Ya ce Murtala Sule Garo gogaggen dan siyasa ne wanda zai taimaka matuka wajen tafiyar da gwamnati.
Haka kuma Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yabawa Majalisar Dokokin Jihar Kano karkashin jagorancin Kakaki, Rt. Hon. Jibril Ismail Falgore, bisa gaggauta tantance Garo .
Ya ce nan ba da jimawa ba za a rantsar da sabon Mataimakin Gwamnan tare da kira ga al’umma da su ba shi hadin kai domin sauke nauyin da ke kansa yadda ya kamata.
Gwamnan ya kuma taya Garo murnar samun amincewar majalisa, sannan ya taya sabuwar Shugabar Ma’aikatan Jihar Kano, Hajiya Bilkisu Shehu Maimota murna bisa sabon mukamin da aka ba ta.
Ya ce irin gudunmawar da ta bayar a matsayinta na Darakta da kuma Babbar Sakatariya a baya abin a yaba ne matuka.
Haka kuma ya bukaci masu ruwa da tsaki da ma’aikatan gwamnati su mara mata baya domin samun nasara a sabon aikin da aka dora mata.
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t