Gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya naɗa Abubakar Ibrahim Matawalle a mai riƙon Babban Daraktan Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar.
Wannan na cikin sanarwar da Daraktan Yada Labaran Gwamnan Kano, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a ranar Litinin 2 ga Fabrairu 2026.
Sanarwar ta bayyana cewa Abubakar Ibrahim Matawalle ya taba rike mukamin Babban Sakataren Hukumar Jin Daɗin Alhazan a baya, tare da rike mukamin babban sakatare a ma’aikatar kula da ma’aikata kafin ritayarsa daga aikin gwamnati.
Matawalle ya yi ritaya daga aikin gwamnati a shekarar 2014, bayan shafe shekaru a matsayin babban sakatare, kuma ya taba jagorantar harkokin aikin hajji a lokuta daban-daban a jihar Kano.
Sanarwar ta ce, naɗin nasa na daga cikin matakan da gwamnatin jihar ke dauka na cike guraben mukamai domin inganta tafiyar da muhimman hukumomin gwamnati, inda sanarwar ta ce nadin ya fara aiki nan take.
Hakazalika Gwamnan ya ƙarawa Yusuf Mukhtar matsayin Permanent Secretary.
Sai Barr. Rahama Malam Alhaji, Provost, Kano State Anti-Corruption Institute.
Jarumar Kannywood Aina’u Ade, itama ta sami ƙarin matsayi daga Special Assistant zuwa Senior Special Assistant, Kanywood Affairs.
Wannan sanarwar ta samu saka hannun babban daraktan yaɗa labaran gwamnan Kano Sunusi Bature Dawakin Tofa a yau Litinin.
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t