Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya tabbatar da cewa gwamnatinsa na kan gaba wajen kafa kwalejin kimiyya da Fasaha a karamar hukumar Gaya, a matsayin wani ɓangare na yunkurin fadada damar samun ilimi na fasaha da sana’o’i a jihar.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa, gwamnan ya bayyana wannan ne yayin kaddamar da rukunin biyu na shirin tallafin karatu ga daliban digiri na biyu daga gida da ƙasashen waje a Fadar Gwamnatin Jihar Kano.
Gwamnan ya ce kafa wannan kwalejin wani muhimmin mataki ne da zai ƙarfafa ilimi na fasaha da sana’o’i, yana mai jaddada muhimmancin koyon ƙwarewa da kirkire-kirkire wajen samar da ayyukan yi da habaka tattalin arziki.
Ya bayyana cewa, da zarar an fara aiki, cibiyar za ta ba matasa a Gaya da kewaye damar samun ingantaccen ilimi da horon aiki wanda zai shirya su don samun aiki mai kyau ko fara sana’a.
Gwamnan ya kara da cewa, kwalejin zai kuma zama cibiyar horo ga masu sana’a da ƙwararru da ke son haɓɓaka ƙwarewarsu da samun takardun shaidar kwarewa, wanda hakan zai taimaka wajen bunƙasa tattalin arzikin jihar.
Ya sake jaddada cewa Gwamnatin Jihar tana aiki tukuru don tabbatar da cewa duk shirye-shiryen da ake bukata sun kammala domin fara aiki cikin sauri.
Gwamna Yusuf ya nuna tabbacin cewa kafa Kwalejin kimiyya da Fasaha ta Gaya zai ƙara wa tattalin arzikin yankin ƙarfi ta hanyar samar da ayyukan yi, bunkasa harkokin kasuwanci, rage hijirar daga ƙauye zuwa birni, da kuma haɓaka ci gaban da ya shafi kowa da kowa.
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t