Gwamn Abba Kabir Yusuf ya amince da kashe Naira miliyan 164 domin cigaba da inganta aikin Asibitin yara na Asiya Bayero da ke cikin birnin Kano.
Kwamishinan yaÉ—a labarai na jihar Kano Kwamared Ibrahim Abdullahi Wayya ne ya bayyana hakan bayan kammala zaman majalisar zartaswa na jihar Kano karo na 33 a yayin da yake karin haske ga manema labarai na fadar gwamnatin Kano.
Wariya ua ce, an amince da kudin ne a zaman majalisar zartaswa kuma an warewa bangaren lafiya kuÉ—i sama da naira miliyan 270 domin gyaran wasu manyan asibitoci ciki harda Asibitin Tiga.
Sannan kwamishinan yace za’a, sabunta kayan aikin jinya, da kuma samar da sabbin dakunan kwana da ofisoshi domin inganta yanayin aiki da karɓar marasa lafiya.
Zaman majalisar zartaswa karo na 33 ya amince a kashe kuÉ—ade sama da naira miliyan dubu 19 domin yin wasu mahimman ayyukan raya kasa da bunkasa bangaren lafiya da Ilimi da samar da ruwan sha da sauransu.
A cewar kwamishinan, matakin ya kasance cikin shirin gwamnatin Abba Kabir Yusuf na farfaÉ—o da cibiyoyin kiwon lafiya a fadin jihar, tare da nufin tabbatar da cewa kowane yanki yana da asibitin da ke ba da kulawa ta zamani.
Wayya yace zaman majalisar ya kuma amince da gina gidaje guda 50 a kowacce karamar hukuma ta wajen birnin Kano domin bunkasa yankunan karkara.
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t