Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya bai wa hukumar Hisbah umarnin daukar mataki kan wasu kungiyoyi da ake zargi da koyar da Luwadi da Madigo a jihar Kano.
Alfijir labarai ta ruwaito umarnin Gwamnan na zuwa ne bayan zargin bullar wasu kungiyoyi dake fakewa da tallafawa makarantu suna yada mummunar dabi’ar auren jinsi a jihar Kano.
Kwamishinan yada labarai na jihar Kano, Baba Halilu Dantiye ne ya bayyana hakan a jiya Lahadi yayin zantawa da manema labarai.
Tun da farko kwamishinan ya ce gwamnatin jihar baza ta amince da auren jinsi ba ko da akwai hakan a yarjejeniyar Samoa da ake zargin Najeriya ta sanyawa hannu.
“Na tattauna da mai girma Gwamna kuma ya nuna rashin jindadinsa da wannan yarjejeniya da aka ce ansa hannu idan ta tabbata hakan ne, kuma ya bada tabbacin wannan ba zai samu gurbin zama a jihar Kano ba, ya yi Alla-Wadai da shi saboda Kano gari ne wanda al’ummarsa kaso 98 cikin dari Musulmai ne, kuma Musulunci bai yarda da wannan ba”.
Dangane da batun kungiyoyi da ake zargi da yada akidun masu aikata Luwadi da Madigo, kwamishinan ya ce sun samu bayanai kan korafe korafen mutane kan lamarin.
” Wannan ma mun yi magana da shi(Gwamna) ya bai wa Hisbah umarni su je su zakulo su kuma duk inda aka samu irin wadannan za a dauki matakin da ya dace don baza mu yarda da a zo a gurbata mana al’ada da addinmun ba”.
Daga karshe, kwamishinan ya ce ana tattaunawa da Malamai don zukulo dabarar da za a kaucewa fadawa wannan lamari a jihar.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj