Gwamnan Kano ya bayyana matuƙar girgiza da alhini bisa rasuwar ‘Yan majalisar dokokin jihar guda biyu da suka rasu a rana guda.

IMG 105115 251225 1766656327102

Gwamnan Kano Alh Abba Kabir Yusuf ya bayyana matuƙar girgiza da alhini mai tsanani bisa rasuwar ‘Yan majalisar dokokin jihar Kano guda biyu da suka rasu a rana guda.

Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya sanya wa hannu a ranar Laraba.

Gwamna Yusuf ya bayyana rasuwar Hon. Sarki Aliyu Daneji, ɗan majalisa mai wakiltar Ƙaramar Hukumar Kano Municipal kuma Shugaban Kwamitin Hajji na Majalisar da kuma Hon.Aminu Sa’adu, ɗan majalisa mai wakiltar Ƙaramar Hukumar Ungoggo kuma Shugaban Kwamitin Kasafin Kuɗi, a matsayin wani baƙin lamari mai raɗaɗi a tarihin Jihar Kano.

Gwamnan ya ce wannan masifa ta jefa gwamnati da al’ummar Kano cikin jimami da baƙin ciki yana mai jaddada cewa rasa ‘yan majalisa biyu masu ƙwazo a cikin sa’o’i kaɗan babban bala’i ne da kalmomi ba za su iya bayyana girman sa ba.

A cewarsa, marigayan sun kasance jajirtattun ma’aikatan gwamnati, amintattun ‘Yan siyasa, kuma ingantattun wakilan al’ummominsu waɗanda jajircewarsu wajen dokoki da wakilcin al’umma ba abin shakka ba ne.

Gwamna Yusuf ya ƙara da cewa Jihar Kano ta yi babban rashi, domin ta rasa ‘Ya’Ya biyu da suka sadaukar da rayuwarsu wajen hidimar jama’a yana mai cewa mutuwarsu ta bar gibi mai raɗaɗi a Majalisar Dokokin Jihar da kuma al’ummominsu.

Ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan marigayan shugabanci da mambobin Majalisar Dokokin Jihar Kano, da kuma al’ummar Ƙananan Hukumomin Kano Municipal da Ungoggo.

Gwamnan ya roƙi Allah Maɗaukakin Sarki (SWT) da Ya gafarta musu kura-kuransu,Ya Kuma lullube su da rahamar Sa, Ya saka su a Aljannatul Firdaus tare da bai wa iyalansu da daukacin al’ummar Kano juriyar jure wannan babban rashi.

Haka kuma Gwamna Yusuf ya yi kira ga al’ummar jihar da su zauna lafiya, su kasance masu haɗin kai da yawaita addu’o’i yana mai bayyana lamarin a matsayin jarrabawa ta imani da haƙuri na bai ɗaya.

An riga an binne marigayi Hon. Aminu Sa’adu a makabartar Ungoggo yayin da za a gudanar da sallar jana’izar marigayi Hon. Sarki Aliyu Daneji da misalin ƙarfe 10 na safe a masallacin fadar Mai Martaba Sarkin Kano a ranar Alhamis.

A ƙarshe, Gwamna Yusuf ya ce, “A madadin gwamnati da al’ummar Jihar Kano, muna miƙa ta’aziyyarmu ga Majalisar Dokokin Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Kakakin Majalisa, Rt. Hon. Jibrin Ismail Falgore, da kuma iyalan marigayan. Allah Ya sa Aljannatul Firdaus ce makomarsu ta ƙarshe, Amin.”

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *