Gwamnan Kano ya biya diyyar Miliyan 642 ga al’umar da zaizayar kasa ta shafa

FB IMG 1746799233462

Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya biya diyyar Naira miliyan 642 ga al’umar da zaizayar kasa ta shafa a yankin Bulbula da Gayawa dake Karamar Hukumar Ungoggo.

Da yake jawabi yayin gabatar da chekin kudin ga al’umar da zaizayar Kasar ta shafa a yankin, gwamna Abba Kabir Yusuf yace gwamnati zata shimfida bututun ruwa tare da cike dukkanin kwazazzabon da ruwa ya zaizai a shimfida kwalta tare da haska titin da fitulu masu amfani da hasken rana.

Ya bayyana rashin jin dadinsa bisa yadda kwazazzabon ya zama mafakar masu aikata miyagun laifuka da gurbata Muhalli da yaduwar cutuka a tsakanin al’uma.

Yace aikin rufe kwazazzabon da shimfida titi a kansa zai lakume sama da naira biliyan 11 wanda gwamnatin jiha hadin gwiwa da bankin duniya zasu gudanar.

Ya yi kira ga wadanda suka samu kudin diyyar da su yi kyakkyawan amfani da su wajen sayen gidaje ko wata kaddara da zata amfanesu da iyalansu a nan gaba.

A nasa bangaren kwamishinan Muhalli Dr. Tahir Muhammad Hashim ya bayyana yadda matsalar zaizayar kasa ta addabi al’umar yankin Bulbula da Gayawa da kuma nau’in mutanen da ma’aikatarsa ta tantance domin biyansu kudin fansar muhallansu.

Zaizayar kasa a yankin Bulbula da da Gayawa ta haddasa mummuar gurbatar Muhalli da karuwar aikata laifuka da ta’ammuli da miyagun kwayoyi  da dakile al’amuran cigaban ilimi da kasuwanci a yankin.

Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news ku shiga nan  👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/KoLt2IMlnQfJPP6zNrcNKD

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *