Kwamati na musamman ya haramta yin shirin Siyasa na kai tsaye a kafafen yada labarai a jihar Kano

IMG 20250508 WA0096

Daraktan aiyuka na musamman na ma’aikatar yaɗa labarai ta jihar Kano, Sani Abba Yola, ne ya sanar da hakan ta cikin wata sanarwa da ya aikewa yan jarida, inda ya ce an dauki matakin ne a yayin wani zaman tattaunawa tsakanin Ma’aikatar yaɗa labaran jihar da kuma shugabannin kafafen yaɗa labarai.

A cewar sanarwar, “Gwamnatin Kano ta dauki matakin ne a kokarinta na magance matsalar cin zarafin al’umma da ake yi a kafafen yada labarai da sunan adawar siyasa, kuma dukkanin Shugabannin kafafen yada labaran sun amince da Wannan matakin tare da yin alkawarin tabbatar da shi a kafafen yada labaransu”.

Sauran matakan da zaman ya cimma sune;

Duk wanda ya zo zai yi hirar siyasa a gidan Rediyo to dole ne ya rubuta takardar alkawarin ba zai ci zarafin kowa ba, kuma ba zai bata sunan kowa ba, haka kuma ba zai yi duk wani abu na kawo hargitsi ba.

Bugu da kari an haramtawa masu gabatar da shirye-shirye yin tambayoyin da za su tunzura wadanda suke hira da su, don gudun kada hakan ya kawo bata suna ko cin zarafin wani.

A karshe kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida na jihar Kano, Kwamared Ibrahim Waiya, ya godewa Shugabannin kafafen yada labaran saboda hadin kai da goyon bayan da suke bawa gwamnatin jihar a koda yaushe.

Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news ku shiga nan  👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/KoLt2IMlnQfJPP6zNrcNKD

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *