Rahotanni sun nuna cewa gadar na daga cikin muhimman hanyoyin zirga-zirga a cikin birnin Kano, amma tana fuskantar matsaloli da suka hada da hatsarurruka masu yawan faruwa, lamarin da ke haddasa asarar rayuka da dukiyoyi.
A yayin ziyarar, Gwamnan ya zagaya wajen tare da rakiyar jami’an gwamnati da kwararrun injiniyoyi, inda ya saurari bayanai kan halin da gadar ke ciki da kuma abubuwan da ke haddasa haɗurran.
Da yake jawabi ga manema labarai, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana damuwarsa kan lamarin, yana mai cewa gwamnatinsa za ta dauki matakan gaggawa domin tabbatar da tsaro a kan gadar da kewaye.
Ya kuma bayar da umarnin a gudanar da cikakken bincike na fasaha domin gano matsalolin da ke janyo hatsarurrukan, tare da daukar matakan da suka dace ciki har da sanya karin alamomin hanya, fitilu, da kuma inganta tsarin zirga-zirga.
Mazauna yankin da masu amfani da hanyar sun jinjina wa wannan mataki na gwamnan, suna mai fatan cewa daukar wadannan matakai zai taimaka wajen rage yawan haɗura da kuma kare rayuka da dukiyoyin jama’a.
Ziyarar na daga cikin kokarin gwamnatin jihar na inganta ababen more rayuwa da tabbatar da tsaron lafiyar al’umma a Jihar Kano.


Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t