Gwamna Kano ya musanta labarin zargin da Dan Bello ya yi na kwangilar da aka ce an bayar a kwanan nan domin samar da magunguna ga kananan hukumomi 44 na jihar.
Alfijir labarai ta ruwaito hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da aka baiwa manema labarai mai dauke da sa hannun kwamishinan yada labarai Baba Halilu Dantiye da sakataren yada labarai na gwamna Sanusi Bature Dawakin Tofa.
Sanarwar ta bayyana cewa Gwamnan ya umurci Shugaban Hukumar karbar Korafe-korafen Jama’a da Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano da ta gaggauta bincikar wannan zargi tare da bayar da rahoton sakamakon da ya dace domin ci gaba da daukar matakin da ya dace.
Gwamna Yusuf ya kuma bukaci al’ummar jihar Kano su yi hakuri har sai an kammala bincike.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj