Gwamnan Kano ya rushe Shugabancin hukumar kare hakkin masu sayan kayayyaki ta Jihar

FB IMG 1723959647845

Gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf, ya amince da rushewar Shugabancin hukumar kare hakkokin masu Sayan kayayyaki ta Jihar Kano wato (Consumer Protection Council) nan take.

Sanarwar ta fito ne daga Sakataren gwamnatin Jihar Kano (SSG), Alhaji Umar Faruk Ibrahim, wanda ya bayyana cewa, matakin ya biyo bayan dogon rikicin shugabanci da ya dabaibaye hukumar, duk da kokarin da aka sha yi wajen tabbatar da zaman lafiya da ingantaccen yanayin aiki a cikinta.

A cewar sanarwar, mai dauke da sa hannun daraktan yada labarai na ofishin Sakataren gwamnatin Kano Malam Musa Tanko yace bisa umarnin gwamnan Shugaban hukumar,da Sakataren Zartarwa da dukkan mambobi, ciki har da mambobin Ex-Officio, rushewar ta shafa nan take.

Sakataren Gwamnatin Jiha ya kuma umurci dukkan jami’an da abin ya shafa da su mika ragamar aiki tare da dukkan kayayyakin gwamnati da ke hannunsu ga jami’in da ya fi kowa girma a hukumar, kafin ƙarshen lokacin aiki a ranar Litinin, 27 ga Oktoba, 2025.

Haka kuma dukkan takardun mika aiki an bukaci a kai su zuwa Ofishin Sakataren Gwamnatin Jiha (Sashen Bincike,da Kimantawa da Harkokin Siyasa) da kuma Kwamishinan Ma’aikatar Zuba Jari da Kasuwanci

Sanarwar ta kuma shaida cewa gwamnatin Jihar Kano za ta ci gaba da daukar matakai don tabbatar da ingantaccen shugabanci, da gaskiya, da kyakkyawan gudanar da aiki a hukumominta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *