Gwamnan Kano ya sauke Buba Galadima daga Shugaban Hukumar Gudanarwar Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Kano.
Hakan na kunshe ne cikin sanarwar da Daraktan Yaɗa Labaran Gwamnan Kano, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a ranar Asabar
Sanarwar ta bayyana cewa Gwamnan ya amince da nadin Sarkin Gaya, Alhaji Dakta Aliyu Ibrahim Abdulkadir, a matsayin sabon Shugaban Hukumar Gudanarwar makarantar.
Ya ce matakin sauke Galadima ya biyo bayan sake fasalin tsarin gudanarwa da daidaita ayyuka da ajandar KanoFirst.
Gwamnan ya gode wa Injiniya Buba Galadima bisa gudunmawar da ya bayar a lokacin da yake rike da mukamin, tare da bukatar sabon shugaban ya yi amfani da kwarewarsa wajen bunkasa harkokin ilimi da gudanarwa a makarantar.
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t