Gwamnan Kano ya taya wasu sabbin shugabannin gidajen Radiyo murnar kama aiki

Abba k Yusuf

Gwamnatin Jihar Kano, karkashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf, ta taya manyan ’yan jarida huɗu murna bisa sabon nadin da aka yi Masu a matsayin Manyan Daraktoci da Manajoji na wasu muhimman tashoshin rediyo a cikin jihar.

Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Kwamishinan Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida, kwanared Ibrahim Abdullahi Waiya, ya fitar kuma aka rabawa manema labarai.

Sanarwar ta bayyana cewa sabbin shugabannin da aka nada sun haɗa da:

Anas Idris Hassan, Babban Manaja na Vision FM Radio Kano;

Garba Ubale Dambatta, Babban Manaja na Pyramid FM Radio Kano;

Mukhtar Abdullahi Birnin Kudu, Babban Manaja na Nasara FM Radio Kano;

Muhammad Musa Mohammed Inya, Manajin Darakta na Hikima FM Radio Kano.

Gwamnatin Jihar, ta hannun Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida, ta mika sakon taya murna gare su a madadin Gwamnati da al’ummar Jihar Kano baki ɗaya.

An bayyana cewa nadin nasu ya dace kuma ya dogara ne akan cancanta da ƙwarewa, ganin irin jajircewar da suka nuna a cikin harkar yada labarai tsawon shekaru.

Gwamnatin ta yaba da gogewarsu da kuma jajircewar su wajen inganta aikin jarida mai ma’ana wanda ya yi daidai da hangen nesa na Gwamna Abba Kabir Yusuf wajen haɓaka aikin jarida na gaskiya, amana, da ci gaba a cikin jihar Kano.

Gwamnatin Jihar Kano ta tabbatar da aniyarta ta ci gaba da ƙarfafa alaƙa mai kyau da kafafen watsa labarai wani mataki da ya taimaka wajen inganta wayar da kai da fahimtar jama’a game da shirye-shiryen gwamnati.

“Fatan mu shi ne kafafen yaɗa labarai za su ci gaba da haɗa kai da gwamnatin jiha wajen bin ka’idojin aiki da kuma inganta aikin jarida mai ƙwarewa.”

“Wannan haɗin gwiwa zai taimaka wajen inganta gudanar da harkokin yaɗa labarai a faɗin jihar, da kuma tallafa wa yaƙi da yaɗuwar ƙarya da bayanan da ba daidai ba.”

haka kuma gwamnatin jihar ta bukaci sabbin shugabannin da su tabbatar sun nuna amincewar da aka basu ta hanyar yin aiki cikin gaskiya, adalci, da amana.

Kazalika gwamnatin ta sake tabbatar da kudirinta, ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf, na ci gaba da tallafawa kafafen yaɗa labarai a matsayin muhimmin abokin haɗin gwiwa wajen gudanar da mulki da kuma hulɗa da jama’a.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *