Gwamnatin Borno Ta Bayar Da Tallafin  N987m Ga ‘Yan Kasuwa 7,716 Da Ambaliyar Ruwa Ta Shafa

IMG 20241208 WA1330

Daga, Muhammad Sani Chinade, Damaturu 

Gwamnatin jihar Borno ta raba N987m ga ‘yan kasuwa 7,716 wadanda ibtila’in ambaliyar ruwa ta shafa a Maiduguri ranar 10 ga watan Satumba.

Injiniya Baba Gujbawu, shugaban kwamitin raba kudaden tallafin, ya bayyana hakan a wajen bikin bayar da takardar shaidar tantancewar da aka yi a Maiduguri.

Gujbawu ya ce kwamitin ya shafe watanni biyu yana tantance tare da raba kayan agaji ga gidaje da abin ya shafa a kananan hukumomin Maiduguri, Jere, da Mafa da kuma ‘yan kasuwa daga manyan kasuwanni tara na jihar.

Ya ce kasuwannin da abin ya shafa sun hada da Kasuwar Gamboru, Kasuwar Monday, Tashan Damboa, Metro Plaza, El-kanemi, Kasuwar Kayan lambu, Kasuwar Kwastam, Kasuwar Ganye ta Moromoro, Bukar Shuibu, da Kasuwar Budum.

Ya bayyana cewa an ware wadanda suka ci gajiyar tallafin ne bisa la’akari da irin barnar da aka samu a kasuwancinsu, wanda ya hada da wadanda suka rasa komai da kuma wadanda kadan ya shafa, inda ya kara da cewa za a shigar da kudaden ne kai tsaye zuwa asusun ajiyar ‘yan kasuwar.

Don haka ya bukaci wadanda suka amfana da su yi amfani da kudaden cikin adalci wajen sake ginawa da fadada kasuwancinsu.

Wakilinmu  ya ruwaito  cewa kwamitin ya kuma mika injinan famfun ruwa guda 500 ga manoman da ibtila’in ya shafa a kananan hukumomin Maiduguri da Jere.

Alhaji Bawu Musami kwamishinan noma wanda ya karbi famfunan ruwan a madadin manoman ya bada tabbacin cewa za’a raba kayan cikin gaggawa ga wadanda suka ci gajiyar shirin noman rani.

Babban abin da ya fi daukar hankali a wajen bikin shi ne gabatar da takardar kudi ga babban Manajan kasuwar Maiduguri, wacce aka fi sani da kasuwar Litinin da shugaban kwamitin ya yi.  

Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news zaku iya bibbiyarmu ta 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *