Nafisat Balogun ta zama mace ta farko da ta tuka jirgi a hukumance

Nafisat Balogun

Hukumar Kwastam ta Najeriya (NCS) ta sanar da mataimakiyar Sufeto ta Kwastam (Pilot) Olanike Nafisat Balogun ta zama mace ta farko da ta tuka jirgi a hukumance.

A wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar ta Kwastam Abdullahi Maiwada ya fitar, ya ce Balogun haifaffiyar garin Kaduna ce kuma ta shiga aikin kwastam a shekarar 2002

Balogun tayi diploma a kan fannin Ticket da Cabin Services, da digiri na biyu a fannin Public Administration daga Jami’ar Ahmadu Bello, kafin daga bisani ta samu takardar shedar tukin jirgi a makarantar Flying Academy da ke Miami a jihar Florida, wadda Hukumar kwastam ta dauki nauyinta.

Ta jaddada nasarar da ta samu a matsayin abin zaburarwa ga mata da suke da burin tukin jirgi.

Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *