Gwamnatin Kano Ta Amince Da Korar Ma’aikatan Lafiya 3 Da Dakatar Da Wasu 3

IMG 20240311 WA0053

Hukumar kula da asibitocin jihar Kano ta amince da korar wasu ma’aikata 3, tare da dakatar da wasu ma’aikatan na  3 babban asibitin Karamar Hukumar Kabo nan take bayan samunsu da lefin Cazar kudade daga Marassa Lafiya da suka Wuce Kima da sauran lefuka.

Alfijir labarai ta rawaito Shugaban hukumar Dakta Mansur Mudi Nagoda ya bayyana hakan jim kadan bayan sanya hannu kan amincewar da hukumar ta gabatar bayan kammala ziyarar da sukayi.

Hakan na kunshe ne ta cikin wata Sanarwa da jami ar yada labarai ta hukumar Samira Suleiman ta sanya wa hannu.

Sanarwar ta kara da cewa Asibitin wanda babban sakataren hukumar da babban darakta na cibiyar yaki da cututtuka masu yaduwa ta jihar Kano (KNCDC) Dr. Muhammad Abbas, da darakta janar na CSACA Dr. Usman Bashir suka ziyarce su gaba daya sun nuna bacin ransu ga abinda ya faru tare da amincewar daukar matakin.

Nagoda ya yi bayanin cewa an kama jami’ai 3 na sashen X-ray suna cajin marasa lafiya 12,000 na gwajin X-ray maimakon farashin asibiti da aka amince da shi na 2,000, kuma babu wata takarda da za ta nuna a matsayin shaidar biyan kuɗin da ke barin wurin don aiwatar da gwajin, lamarin da yasa ake X-ray 10 kacal a kowanne mako duk da cewa Injinan Asibitin na X-ray 2 suna aiki. Nan take aka amince da korar jami’an 3.

Har ila yau, shugaban Hukumar ya amince da dakatar da akawun asibitin da mai binciken kudi da shugaban dakin gwaje-gwaje saboda sayar da kayan gwajin cuta mai karya Garkuwar jikin dan adam wanda kyauta gwamnatin jihar ta ba wa cibiyoyin, kuma an umarce su da su kai kansu ga hedikwatar hukumar don ci gaba da ladabtar da su.

Bugu da kari, Dakta Nagoda ya bayyana cewa dakin karbar Haihuwa na Asibitin ba shi da tsari domin ba shimfidar gado a kan gadaje, babu wani jami’in kula da gurin, haka kuma an wulakantar da wasu kayayyakin kula da lafiyar Alumma wanda wani Dan majalisa ya bayar da gudummawar shekaru 4 da suka gabata, tare da nuna halin ko in kula da kayayyakin yaki da cutar COVID-19.

Shugaban ya kuma ce abin bakin ciki ne bayan gwamna Abba Kabir Yusuf ya tabbatar da cewa ya dawo da kowane ma’aikacin lafiya a kan ma’aunin albashin CONHESS, amma duk da haka suna cin zalin Marasa Lafiya.

Sanarwar ta ce shugaban ya yi kira ga Ma’aikatan hukumar da su rika gudanar da ayyukansu don cigaba da kula da lafiyar Alummar Kano.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/CJ2q8cmhhOxFY6OEgwV5vk

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *