A wani gagarumin mataki na gyara tsarin biyan albashi a cikin jihar, Gwamnatin Jihar Kano karkashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf, ta cimma wata babbar nasara a kokarinta na tsaftace harkokin albashi a ma’aikatun gwamnati.
A cikin wannan tsari na gyare-gyare, an kafa Kwamitin Duba Albashi (Pay Parade Committee), wanda zai fara aiki nan ba da jimawa ba. A shirin fara cikakken aiwatar da aikinsa, Kwamitin ya ga dacewar hada kai da dukkan masu ruwa da tsaki. Saboda haka ne Kwamitin ya buga takardun biyan albashi na watan Maris, 2025, sannan ya bukaci dukkan Ma’aikatu, Hukumomi, Cibiyoyi da Kananan Hukumomi da su tantance takardun albashin tare da bayyana duk wata matsala da suka lura da ita, a matsayin shiri na gudanar da cikakken binciken albashi da za a kaddamar a ranar Litinin, 28 ga Afrilu, 2025.
A yayin tantancewar da aka gudanar, an gano wata babbar matsala a cikin tsarin biyan albashi na Kananan Hukumomi, inda aka bayyana cewa mutane 247 da suka riga suka yi ritaya ko kuma suka rasu, har yanzu ana ci gaba da biyansu albashi. Wannan dabi’ar ta haifar da asarar kudi har naira miliyan 27,824,395.40 a watan Maris, 2025 kadai.
A cikin gaggawa kuma cikin kwarewa, Gwamnati ta mayar da kudaden zuwa baitul malin Kananan Hukumomi, duk da cewa ana ci gaba da gudanar da cikakken bincike domin gano girman wannan badakala da kuma wadanda ke da hannu a ciki.
Wannan nasarar dawo da kudaden wata alama ce ta jajircewar wannan Gwamnati wajen tabbatar da gaskiya, adalci da kuma amintaccen tafiyar da dukiyar jama’a.
Gwamnati tana nan daram a kan kudurinta na tsabtace tsarin biyan albashi daga duk wata barna. Wadanda aka samu da hannu a cikin wannan danyen aiki za a bankado su, sannan a hukunta su bisa tanadin doka.
Musa Tanko Muhammad
Sakataren Watsa Labarai
Ofishin Sakataren Gwamnatin Jihar Kano (SSG)
Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news ku shiga nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/KoLt2IMlnQfJPP6zNrcNKD