Gwamnatin Kano Ta Ci Gaba Da Rushe Rushe A Daren Lahadi

Alfijir Labarai ta rawaito Yadda Gwamnatin jihar Kano ta ci gaba da rushe gine-ginen da ke cikin filin Masallacin Idi na Ƙofar Mata.

Motocin Rusau huɗu ne suka ci gaba da rushe gine-ginen Shaguna ɗari da aka yi a cikin filin idin.

Shugaban hukumar tsara birane ta Kano Arch. Ibrahim Yakubu ya shaida wa Freedom Radio cewa abin takaici ne ace an gine filin Babban Masallacin Idi na garin Musulunci.

Ya kuma yi kira ga waɗanda ke da kayayyaki a wuraren da aka sanya wa jan fenti da su gaggauta kwashewa, domin ci gaba da wannan rushe-rushen ya zama dole ba gudu ba ja da baya a cewarsa.

Freedom Radio

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Alfijir Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/GdLiqZyHuSz5NhjdGoGRGZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *